8 Faburairu 2021 - 12:16
An Soke Babban Zaben Somaliya Saboda Kasa Fahimtar Juna

An Somaliya an soke babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin.

ABNA24 : An dage zaben ne har zuwa wani lokacin da ba a tantance ba, sakamakon rashin samun fahimtar juna, tsakanin gwamnatin tarayya da kuwa wasu jihohin kasar.

Shugaban kasar dai ya zargi wasu jijojin kasar biyu daga cikin biyar da kawo tarnaki a zaben.

A gobe Litinin 8 ga wata ne ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissu da aka shirya gudanarwa.

Soke zaben da aka yi zai bai wa Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo damar ci gaba da jan ragamar mulkin kasar duk kuwa da cewa sauran kwanaki 6 kachal wa'adin mulkinsa ya kawo karshe.

Dama dai Farmajon na cikin jerin 'yan takara da ke zawarcin kujerar shugaban kasar na wani wa'adin shekaru 4 nan gaba.

Somaliya ta kwashe shekaru sama da 30 ba ta gudanar da zaben gama gari ba, inda wasu kwamitin amintattu na kasar ne mai mambobi 51 ne ke zaben shugaban kasa.

342/